Na daina zuwa Coci saboda Faston kullum zagin Buhari yake yi, Femi Adesina

Jummaʼa, Nuwamba 05, 2021

Mai magana da yawun Shugaban kasa ya daina zuwa cocinsa saboda Malamin cocin na zagin Buhari
Femi Adesina ya bayyana cewa shekarunsa talatin yana zuwa wannan coci amma saboda haka sai ya yanke shawaran daina zuwa
Adesina ya kasance mai magana da yawun shugaban kasa tun lokacin da Buhari ya hau mulki a 2015
Abuja – Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana yadda ya daina zuwa Coci ranar Lahadi a Abuja saboda Faston na zagin Shugaba Muhammadu Buhari.
Adesina a jawabin da ya saki ranar Alhamis ya bayyana hakan.
A jawabin da ya yiwa take, ‘Kumuyi fa daban yake’, ya jinjinawa Fasto Williams Kumuyi na Deeper Christian Life wanda ya ce mutane su daina zagin Buhari.
Adesina, duk da cewa bai bayyana sunan cocinsa ba, an gano cewa mamban Cocin Foursquare Gospel ne inda ya kasance yana zuwa tun 1988.
A jawabin, mai magana da yawun Shugaban kasan yace wasu Fastoci sun mayar da mimbarin wa’azi wajen zage-zage da yada kiyayya.
Yace: “Na kasance ina zuwa wani Coci a Abuja daga 2015 zuwa 2018, kawo zuwa lokacin da Faston ya fara ganin kansa a matsayin wanda zai kawo karshen gwamnan Shugaba Buhari.”
“Kowace Lahadi, zage-zage da soke-soke yake yi. Amma nayi hakuri, tun da na fi shekaru talatin ina zuwa Cocin. Sai ranar da abin ya isheni.”
Adesina ya ce lokacin da aka sace daliban makarantan Dapchi, babu irin sunan da Faston bai kira shugaba Buhari da shi ba, amma da aka sako daliban bai ce komai ba.
legit.hausa.ng
Recent Comments