Hukuncin Haduwar Azumin Arfa da Ranar Juma’a
Wasika zuwa ga Ass Prof Muhd Sani R/Lemo
Asslamu Alaikum,
Da fatan Malamina ya tashi lafiya!!
Malam kwatsam ina cikin laluben abinda zan amsawa Wassu bayin Allah kan yanda naga sun rikice kan yadda wassu maganganu suka rudasu kan takamaimai din zance kan wannan Mas’alar ina cikin tattauna abinda zan amsa musu sai i sakonka ya fado min a lalitar Whasapp dina dauke da muryarka da ba za ta iya buya min ba kana bada gamsashshiyar amsa kan wannan mas’ala ta Ilimi.
Malam na saurara na fahimta, a takaice dai ka tattauna wadannan gabobi cikin wannan takaitaccen sakon murya da ka aikawa dalibanka gabanin sauran Mutane, cikin sakon;
(1) Ka ambato Hadisan Falalar tsayuwar Arfa da suka gwada azumtar Ranar Arfa ga mazauna gida yana kankare zunuban shekarar data gabata da shekara mai zuwa.
(2) Fayyace ranayakun Juma’a, Ranar Arfa, Ranakun Sallar Layya a matsayin ranakun bukukuwan Musulmai ne.
(3) Hanin da Annabi yayi na kar a kebe ranar Juma’a ko darenta da Azumi bai shafi Azunzuma na Musamman da ke fadowa a irin wannan rana ba, Ka buga Misali da Azumin Arfa da na Ashura dss.
(4) Ka ce ba wai dole ne sai Mutum ya hada da Alhamis ba in zai azumci ranar Arfa idan ta fado a ranar Juma’a.
(5) Ka ambata cewa Wannan zance da na ambta a namba ta (4) shine abinda Ibnu Qudama(Masani kan tantance zantukan Malamai da sabaninsu) da kuma Ibnu Hajar (Masani kan tantance ruwayoyi hadisai da ingancinsu) da kuma Sheikh Bin Baz(Malamin da duniyar Musulmin yau suka shaidi iliminsa da taqawarsa) suka tabbatar.
Malam na tabbata ka takaita ne don sakon ya zamo gajere mai saukin saurara.
(6) Malam kayi nuni kan kara dagewa don Ribatar azumtar ranar Arfa irinta wannan shekarar (1443/2022) ga Mazauna gida da Mahajjata don samuwar wani lokaci da ke ranar duk Juma’a bayan La’asar da ba musulmin da zai daga hannu yana rokon Allah cikinsa sai an biya masa bukatarsa. Shikenan ga azumi ga lokacin addu’a a ranar Juma’a!!
Malam Bayani ya fito!!
Malam ashe saura kadan wassu bayanai su rudi wassu su bari wannan damar ta haduwar Arfa da Juma’a ta kubuce musu sakamakon daukar bayan duniyar Gizo da rashin tuntubar Malamai.masu warware zare da abawa da kuma tantance kwaya da tsakuwa.
Sai a nemi Audio na musamman da ka yi shi a wanan litinin 5/12/1443/// 4/07/2023
Almajirinka
Ibrahim Adam Omar Disina
Makkah 6/12/1443